Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Syria Ta Tsagaita Kai Hari Birnin Aleppo


Irin barnar da yaki yayi a Aleppo dake Syria

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov, yace gwamnatin Syria ta dakatar da duk wasu matakan soji a gabashin birnin Aleppo, gabannin wata ganawa tsakanin kwararru ta fuskar soji na Amurka da Rasha, dangane da halin da ake ciki a birnin da yaki ya daidaita.

Tunda farko a jiya Alhamis, sakataren harkokin wajen Amurka John kerry, yace "yana da tsammanin" zata yi wuya a cimma tsagaita wuta da kasar Rasha na kawo karshen fada a Aleppo.

Bayan da suka gana da Lavrov a binrin Hamburg jiya Alhamis, Kerry ya gayawa manema labarai cewa yana dakon "wasu bayanai da shawarwari"," ya kara da cewa "muna aiki kan wani abu a nan" ba tareda ya bada karin bayani ba.

A binrin New York, jakadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan rikicin na Syria, Staffan de Mistura, yayi marhabin lale da sanarwar da Rasha ta bayar, duk da haka ya gayawa manema labarai cewa bashi da masaniyar ko an daina yaki, kuma ko an kwashe farar hula ba.

Majalisar Dinkin Duniya zata halarci taron da za'a yi gobe Asabar tsakanin manyan kasashen dangane da wannan rikici. Za'a yi ganawar ce a birnin Geneva.

Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG