Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ta’azzarar Danniya a Nicaragua


Amurka ta kakaba takunkumi ma wasu kusoshi hudu na gwamnatin Ortega-Murillo a Nicaragua, yayin da guguwar takura da tursasawa a kasar ta kai wani sabon mizani.

Wadannan kusoshin gwamnatin sun hada da wakilai daga majalisar dokoki ta kasa, bangaren banki, sojoji, da kuma 'yar Daniel Ortega da Rosario Murillo.

'Yan watanni kawai kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba na 2021, an kame manyan shugabannin adawa 27, ciki har da 'yan takarar shugaban kasa shida kan zargin cin hanci da rashawa da kuma batun tsaron kasa.

Sun hada da Cristiana Chamorro, Arturo Cruz, Felix Maradiaga, Juan Sebastian Chamorro, Miguel Mora, Medardo Mairena da shugabannin ɗalibai, wakilan kamfanoni masu zaman kansu, da sauran masu fafutuka na farar hula. Gwamnatin ta ci gaba da musguna wa kafofin yada labarai masu zaman kansu da sauran mambobin kungiyoyin farar hula wadanda ke nuna rashin amincewarsu su ma.

A cikin wata rubutacciyar sanarwa, Sakataren Harkokin Wajen, Antony Blinken ya yi Allah wadai da matakan gwamnatin Ortega-Murillo na baya-bayan nan kuma ya bayyana cewa Amurka “ta dora alhaki kare lafiyar mutanen kan Shugaba Ortega da wadanda aka hada baki da su a wannan aika aikar.”

Takunkumin na Amurka, an kakaba su ne saboda matsin lamba na baya-bayan nan, da kuma gazawar gwamnati wajen aiwatar da sauye-sauye masu ma'ana a tsarin zabe da Kungiyar Kasashen Nahiyar Amurka ta bukaci a yi da goyon bayan Kwamitin Kare Hakkin Dan-Adam na Majalisar Dinkin Duniya.

Yayin da wannan sabon mataki na tsoratarwa da danniya ke da matukar muni, cin zarafin da gwamnatin Ortega ke yi wa 'yancin dan adam da dimokiradiyya ba sabon abu ba ne. Wani mummunan murkushe zanga-zangar rajin dimokaradiyya da gwamnati ta yi a shekarar 2018 ya yi sanadin mutuwar a kalla mutane 325; yayin da fiye da 2000 su ka ji rauni; kuma an tsare, an azabtar tare da batar da ɗaruruwan mutane ba bisa ka'ida ba.

Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka Ned Price ya ce “a karkashin Shugaba Ortega, Nicaragua ta zama saniyar ware a duniya tana ta nisantar tsarin dimokiradiyya.” Mista Price ya lura cewa Amurka "tana da karin wasu hanyoyi na ganin an ladabtar da kusoshin gwamnatin da ke daure masu gindi, kuma ba za mu yi jinkirin yin hakan ba."

A ranar 15 ga watan Yuni, kasashe mambobin kungiyar kasashen Nahiyar Amurka su 26 sun goyi bayan kudurin da ke kira ga Shugaba Ortega da ya dauki matakin gaggawa don a koma cikakken mutunta hakkin dan Adam da kuma samar da yanayin gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci. A ranar 22 ga watan Yuni, gwamnatoci 59 sun rattaba hannu kan wata sanarwar hadin gwiwa a kwamitin kare hakkin bil adama na Majalisar Dinkin Duniya inda suka yi kira da a gaggauta sakin fursunonin.

Hobbasar da Amurka ta yi a fannin diflomasiyya ta haɗa da aiki tare da OAS, EU, da sauran abokan hulɗar ƙasa da ƙasa don matsa wa gwamnatin Ortega-Murillo ta sassauta danniyar da ta ke yi wa mutanen Nicaragua, waɗanda su ka cancanci abin da ya fi kasa mai jam'iyya guda.

XS
SM
MD
LG