Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ta Tabbata Ibrahim Gambari Ya Maye Gurbin Marigayi Abba Kyari


Fadar Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da rade-radin nada Ibrahim Agboola Gambari a matsayin sabon shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar.

Farfesa Gambari ya gaji mukamin marigayi Abba Kyari, wanda Allah Ya yi wa rasuwa a watan da ya shige bayan kamuwa da cutar COVID-19.

Farfesa Ibrahim Agboola Gambari dan Asalin birnin Ilorin na jihar Kwara, ya yi karatu mai zurfi ya kuma ya rike mukamai da dama.

Wannan matsayi na mai fada aji a fadar shugaban kasa na da matukar muhimmanci gannin shi ke da alhakin sanya lokaci na ayyuka da kuma wanda shugaban kasa zai iya gani a ko da yaushe har ma da inda shugaban kasar zai je.

Yanzu haka hankali ya karkata ga ganin irin matsayi da salon takun sabon shugaban ma’aikatan na fadar shugaban kasa, la'akari da karfin ikon da marigayi nAbba Kyari yake da shi sa'adda ya ke a kan mukamin.

Saurari Karin bayani cikin sauti daga Shamsiyya Hamza Ibrahim.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:38 0:00


Facebook Forum

XS
SM
MD
LG