Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaddamar Da Ke Faruwa A Majalisar Wakilan Najeriya


Dambarwar siyasar Majalisar Dokokin tarayyar Najeriya.

Yanzu haka dai ‘yan siyasa na ci gaba da bayyana ra’ayinsu kan bukatar hukumomin binciken cin hanci da rashawa su fito da gaskiyar takaddamar zargin aringizon kudi ko cushe a Majalisar Wakilai kan kasafin kudin Najeriya na bana.

Wannan na faruwa ne dai dai lokacin da bangarorin Majalisar masu sabanin ra’ayi kan bayyana cewa wannan ne da gaskiya, ko wancan bashi da gaskiya. Sai dai kakakin Majalisar Wakilai Yakubu Dogara, yace ba wani laifi da shugabannin Majalisar suka aikata kan batun, don haka ba zai amsa kiran wasu da suke neman ya yi murabus ba.

A lokacin da ‘yan jarida ke yiwa Dogara tambaya kan wannan takaddamar a fadar shugaban kasa, yace, “na karanta ka’idar shari’a kuma ni ‘dan Majalisa ne, ban san inda aka ce cusa wani abu a kasafin kudi laifi ba ne, ku ‘yan jarida sai kuje ku bincika.”

Dogara ya kara da cewa ba ya cikin wata damuwa, kuma ba shi bane shugaban kwamitin ladabtarwa na Majalisa ba balle ya fadi cewa za a hukunta ‘dan Majalisa mai wannan zargi Abdulmuminu Jibrin, ko ko a’a.

Daga batun kotun ‘da’ar ma’aikata kan shari’ar shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki, zuwa wannan takaddamar ta Majalisar Wakilai, hakan na kawo cikas ga nasarar aikin Majalisar Dokokin Najeriya ta Takwas.

Saurari cikakken rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya daga Abuja.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG