Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Uwargidan Shugaban Najeriya Ta Fadi Dalilin Kai Gwamnan Ekiti Kotu


Uwargidan Shugaba Muhari Na Najeriya, Aisha Muhammadu Buhari tare Da Ibrahim Ahmed Na Nan Muryar Amurka, August 5, 2016

Daya daga cikin kwakwazon gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose shine, na batanci ga uwargidan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari wato Aisha Buhari, inda yace ba zata iya shiga Amurka ba a halin yanzu.

Bisa dalilin da ya bada na cewa tana da hannu a wata badakala a nan Amurka. Sai kuma gashi ta shigo Amurka a makon da ya gabata wanda har kawo yanzu tana nan a cikin Amurkan.

Inda ta halarci taron da wata cibiyar wanzar da zaman lafiya wato US Institute of Peace ta shirya. A yau kuma tana halartar wani taron da ake gabatarwa na kungiyar ‘yan arewacin Najeriya mazauna Amurka ta Zumunta USA.

Taron da kungiyar ta shirya don gano hanyoyin da za’a bi a taimakawa Najeriya wajen inganta rayuwar al’umma da siyasa. Abokin aikinmu Ibrahim Ahmed ya tattauna da ita a nan cikin sashen Hausa na Muryar Amurka.

Ga tattaunawarsu nan a makalar sautin kasa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

XS
SM
MD
LG