Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaddamar Tantance Mace a Matsayin Kantomar Karamar Hukuma a Kano


KANO: Dr. Abdullahi Umar Ganduje gwamnan Kano

Majalisar dokokin Kano ta jingine batun nada Hajiya Binta Fatima Yahya mace guda daya tilo dake cikin jerin mutane 44 da gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ke muradin nadawa mukaman kantomomi bayan da wa’adin zababbun shugabannin kananan hukumomin jihar ya kare a watan jiya.

Majalisar dai ta amince da mutane 32 daga cikin 44 yayin da tayi watsi da mutane 3 saboda rashin cancantarsu, sai kuma guda 9 da ta jingine batun tantancesu sai an zurfafa bincike akansu.

Hajiya Binta Fatima Yahaya, wadda ke da digiri biyu akan fasahar taswirar gine-gine, ma’aikaciyace a jami’ar kimiyya da fasaha ta jihar Kano dake garin Wudil, kuma tana daga cikin wadanda Majalisar Dokokin ta Kano ta ce nada alamar tambayoyi game da cancantar zama kantomar karamar hukuma.

Hakan dai na zuwa a dai dai lokacin da al’umma ke cewa Majalisar ta yi watsi da jerin mata guda bakwai da gwamnan Kano ya mika mata saboda kyamar da ‘yan Majalisar ke yi na nada mata akan kujerar shugabancin karamar hukuma a Kano.

Amma shugaban Majalisar Hon. Yusuf Abdullahi Ata, ya ce a karamar hukumar Nasarawa ne kawai aka tura musu da sunan mace, wadda itama ta gurfana gaban Majalisa kuma aka samu takaddama cikin takardun da ta bayar, wanda sai an binciki abubuwan da ta gabatar.

Lamarin dai na zuwa ne a dai dai lokacin da kungiyoyin mata ke kokawa akan karancin adadin mata a jerin sunayen kantomomin.

Domin karin bayani saurari rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:01 0:00

Facebook Forum

Bidiyo

Yadda Wani Mutum Ya Mari Shugaban Faransa Emmanuel Macron
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:37 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Marigayi TB Joshua
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Gidajen Rediyon Najeriya Sun Gana Da Jami'an Diplomasiyya Kan Rikicin Twitter
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG