Accessibility links

Takalar Talauci Ne Zai Kawo Zaman Lafiya A Najeriya - inji Bafarawa


Former Sokoto State governor Attahiru Bafarawa and presidential aspirant under the opposition Action Congress of Nigeria, arrives for the Party primary in Lagos, Nigeria. Nuhu Ribadu Nigeria's former anti-corruption czar, who won international acclaim for

Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, kuma Garkuwan Sakkwato, Alhaji Attahiru Bafarawa yace talauci ne babban makasudin tashe-tashen hankulan da ake fama da su a arewacin Najeriya, kuma warware wannan talauci na daya daga cikin muhimman hanyoyin maganin barazanar tsaro da ake fama da shi a halin yanzu.

Dan jam’iyyar ANPP wadda zata hada kai da sauran jam’iyyun adawa domin hada babban jam’iyyar adawa ta ACN, yace girke sojoji da ‘yan sanda da ake yi akan tituna, suna saka mutane suna bude kofofi, ba zai samar da masalahan da ake nema ba.

Da kuma yake bayani kan batun afuwa, Bafarawa yayi wata tambaya irin wadda Shugaba Goodluck Jonathan yayi a baya, yana mai tambayar ko su waye Boko Haram.

Tsohon Gwamnan ya lissafa ire-iren Boko Haram.

Yace “Akwai Boko Haram na talauci, akwai Boko Haram na rashin adalci, akwai Boko Haram na ta’addanci, akwai Boko Haram na Malam Yusuf dake Maiduguri da Yobe.”

Talauci duk yana damun wadannan kungiyoyi in ji Mr. Bafarawa, sannan ya rufe da cewa adalci da maganin talauci ne kawai zai kawo zaman lafiya a arewacin Najeriya.

Ya tattauna ne da wakilin Muryar Amurka, Bello Habeeb Galadanchi.

XS
SM
MD
LG