Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tallafawa 'Yan Gudun Hijarar Najeriya Da Nijar a Diffa Ya Yi Wuya


Wasu Daga Irin Makaman Da Ake Kwacewa Daga Hannun 'Yan Boko Haram

Gudun hijira yana daya daga matsalolin duniya sakamakon rikice rikicen da ke da nasaba da yake-yake ko kuma ayyukan ta'addancin kungiyoyi. Yankin Diffa na Jamhuriyar Nijar na daya daga sansanonin 'yan gudun hijirar da yake ciwa jama'a tuwo a kwarya.

Yankin Diffa a Jamhuriyar Nijar yana taka rawar daukar dubban ‘yan gudun hijira da suka hada da ‘yan Najeriya da Nijar din, wannan sansani dai na wucin gadi na kan babbar hanyar gari-gari ne na kasar. Hanyar na da matukar zafin rana kasancewa kasa ce a cikin sahara sannan ga kwalta a shimfide akan titin.

Mataram kodogo wata ‘yar Najeriya ce da ta tserewa harin Boko Haram da kuma iso wannan sansanin da ke Diffa. Tace, “wata rana ne da misalign karfe 2:30 na dare maharani suka dirarwa kauyen nasu tare da fara harbi da karkashe mutane.

Inda kowa ya yi ta kansa, mutane suka dinga ficewa ba tare da sa ko sutura ba kasancewar dare ne don gudun tsira. Itama tace tuni ta saba danta na goye ta kuma cafi na cafa ta tsere, wanda a yanzu tana tare da ‘ya’yanta guda 8 a wajen.

Majalisar Dinkin Duniya tace bada tallafi ga ‘yan gudun hijirar na Diffa yayi wahala saboda warwatsuwarsu a bangarorin kan babbar hanyar da suka watsu kusan da tazarar kilomita 30 daga nan zuwa can.

XS
SM
MD
LG