Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan takarar jam'iyyar Republican sun fafata tsakaninsu


'Yan takaran jam'iyyar Rpublican. Daga hagu Rubio, da Trump, da Cruz da Kasich
'Yan takaran jam'iyyar Rpublican. Daga hagu Rubio, da Trump, da Cruz da Kasich

‘Yan takarar neman shugabancijn Amurka a karkashin jam’iyyar Republican sun yi ta jefa zafafan kalamai a junansu yayin wata muhawara da aka yi a daren jiya Alhamis.

Wannan lamari ya kara nuna karara yadda ake ci gaba da samun rarrabuwar kawuna a tsakanin jam’iyyar yayin da ake shirin tunkarar zabe a karshen shekarar nan.

A lokacin muhawarar, Sanata Marco Rubio da ya fito daga jihar Florida da Sanata Ted Cruz da ya fito daga jihar Texas da kuma gwamnan Ohio John Kasich, sun yi ta caccakar hamshakin mai kudin nan Donald Trump, wanda ke ci gaba da samun nasara a yunkurinsa na wakiltar jam’iyar a zaben mai zuwa.

Muhawarar wacce ta gudana a birnin Detroit da ke arewacin Amurka, ta nuna yadda ‘yan takarar suka yi ta jefa zafafan kalamai marasa dadi, kamar yadda ake gani a yunkurin neman tikitin wakiltar jam’iyyar ta Republican.

‘Yan takarar sun kuma ta zargin juna kan wanda ya fara furta kalaman batanci a jawaban da suka yi a baya.

XS
SM
MD
LG