Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tarayyar Turai Da Japan Sun Bayyana Damuwa Ga Harajin Da Amurka Zata Dorawa Karafe


Donald Trump-Shugaban Amurka
Donald Trump-Shugaban Amurka

Tawagar cinikayya ta kasar Japan da ta Tarayyar Turai sun gana da takwararsu ta Amurka a jiya Asabar, a wani kokarin kawar da yakin cinikayya a kan niyar shugaban Amurka Donald Trump na dora kudin fito a kan tama da farin karfe.

A ganawar tasu, wakilin Amurka Robert Lightizer da kwamishinan cinikayya ta Tarayyar Turai Cecilia Malmstrom da takwararsu na kasar Japan Hiroshige Seko sun tattauna a kan yanda bangarorin zasu yiwa juna adalci a huskar kasuwanci.

Tarayyar Turai ta fada a wata sanarwa cewa ita da Japan suna da matukar damuwa a kan wannan kudin fito na Amurka. Manyan kasashen masu tasiri, kuma manyan abokan kasuwancin Amurka sun bukaci a fiddasu daga wannan kudin fiton.

Jim kadan bayan tattauanawar, Malmstrom, ta dora a kan shafinta na Tweeter cewar babu alama ko Amurka zata fiddasu a cikin batun harajin, don haka tattaunawa zata ci gaba a mako mai zuwa.

Shiko Seko mai wakiltan Japan, ya fada a wani taron manema labara bayan ganawar, yace yayi tsayin daka kuma ya bayyana matsayinsa cewa wannan batu abin takaici ne, ya kuma ce wannan abu zai yi mummunar tasiri a kan bakin dayan tsarin huldan cinikayya.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG