Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Fidda Gwani na Jam'iyyar APC a Legos


APC
APC

A yau ne Jam’iyyar PDP da APC ke gudanar da taron fidda gwani na dan takarar shugaban kasa.

Wakilinmu Hassan Umaru Tambuwal wanda ya halarci taron fidda gwani na APC a Legos, ya bayyana mana cewar haryanzu dai ba’a fara zaben ba amma an jejjera akwatunan zabe kuma jami’an tsaro na ‘yan sanda na tsaresu, amma ba’a faraba.

Ya kuma ce akwai makada acikin tsakiyar filin wasan na Teslim Balogun dake unguwar Surulere na inda za’ayi zaben share fage na dan takarar jam’iyyar APC.

Ana sa ran za’a fara zaben karfe biyar zuwa karfe shidda na yammacin yau, akwai dai jiga-jigan jam’iyyar zaune, sauran kuma na cigaba da shiga filin zaben.

A yanzu haka dai babu dan takara ko guda daya a filin zaben, ‘yan takarar dai sun hada da janaral Muhammadu Buhari, Sam Nda Isaiah, Turakin Adamawa Atiku Abubakar, Gwamnan Jihar Imo Rochas OkoRochas, sai mai girma gwamna Rabi'u Musa Kwankwaso. Duk cikinsu dai babu wanda ke cikin filin zaben tukunna.

XS
SM
MD
LG