Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Wani Taron Kara Wa Juna Sani Tsakanin Mabiya Addinai a Kaduna


Taron zaman lafiya a Kaduna
Taron zaman lafiya a Kaduna

Ganin yadda ake yawan samun ayyukan ta'addanci da kai hare-hare a wasu yankunan Najeriya ya sa cibiyar wanzar da zaman lafiya da ke Kaduna shirya wani taron kara wa juna sani na malaman addinai. 

A taron na kwanaki uku inda aka tattauna hanyoyin neman maslaha game da abubuwan da ke kawo rikice-rikice da kuma hare-hare a tsakanin al'umma, an cimma matsayar yada fahimtar juna tsakanin mabiya addinai a Najeriya.

Jagoran cibiyar da ta shirya wannan taron, Pastor James Mobel Wuyeh, ya ce dalilin da yasa suka shirya wannan taron shine domin a ja hankalin malamai masu koyarwa a islamiya, da majami'u da manyan malamai akan yadda zasu rinka sarrafa magana da taka burki ga wadanda suke so su wuce iyaka ko kuma suke da tsattsauran ra'ayin addini, da kuma sanin irin lafazin da ya kamata su yi amfani da shi wajen jan hankalin wadanda suka riga suka yi nisa.

Pastor James ya kuma yi kira ga malamai da su koyar da darussa wadanda zasu hana mutune shiga yanayin wuce gona da iri da sunan addini ko a bangaren kabilanci ko na siyasa.

Mahalarta wannan taron da aka yi a jihar Kaduna sun ce irin wanna taron ka iya dinke barakar da ke tsakanin wasu mabiya addinai. Imam Tukur Al-munnar na daga cikin wadanda suka halarci taron, ya ce jama'a sun yi nisa ga juna saboda fadace-fadace ya kuma yaba da taron.

A nasa bangaren, daya daga cikin malaman addinin Kirista, Rev. Mailafiya Shadalafiya, ya ce wannan taro ya kayatar matuka kwarai domin ya ja hankalin jama'a, ya kuma ce an ja hankalinsu akan su fadakar da mabiyansu game da muhimmancin zamanfiya.

Dama dai wasu masana harkokin tsaro na ganin dole ne al’uma su rinka shinfida shirin fahimtar juna don magance matsalolin tsaro maimakon zuba wa gwamnati ido a duk lokacin da rigima ko wani rikici ya taso.

Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00


Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG