Accessibility links

Taron Kungiyar Commonwealth ya soke wata tsohuwar al'adar da ta shafi sarauta

Taron kolin shugabannin kasashen renon Ingila

Kasashen renon Ingila dake halartar taron kolin kungiyarsu ta Commonwealth a kasar Australiaya sun soke wata tsohuwar al’adar da aka dade ana amfani da ita, inda sai ‘ya’ya maza ne kawai, ba mata ba, suke iya gadon iyayensu sarakuna a kan gadon sarauta, ko da kuwa mace ce take gabam mazan a haihuwa.

A jiya jumma’a ne shugabannin kasashen suka cimma wannan yarjejeniya a taton da suke gudanarwa a birnin Perth na Australiya. Haka kuma shugabannin 16 na Commonwealth wadanda Sarauniya Elizabeth ta Ingila ke wa jagora, sun soke ka’idar nan da ta haramtawa masu jiran gadon sarauta auren duk wani ko wata da suke mabiya darikar Katolika.

Tun lokacin da aka daura auren Yarima Williams, mai jiran gadon sarautar Ingila da Kate Middleton, aka soma nazarin wadannan ka’idoji na auratayya.

XS
SM
MD
LG