Accessibility links

Wata sabuwar zanga zanga ta sake barkewa a kasar Turkiya


Masu zanga zangar kin jinin kungiyar kishin Islama ta Ennahda a kasar Tunisiya dake neman kafa gwamnatin hadin guiwa.

Wata kazamar zanga zanga ta sake barkewa a garin kasar Tunisiya inda ya kasance tushen zanga zangar kasashen Labarawa.

Wata kazamar zanga zanga ta sake barkewa a garin kasar Tunisiya inda ya kasance tushen zanga zangar kasashen Labarawa.

Zanga zanga ta barke a birnin Sidi Bouzid jiya Jumma’a, ta tada kayar baya kan jam’iyar Ennahda da aka zaba kwanan nan. Kafofin sadarwa sun laburta cewa, jami’an tsaro sun yi harbi a iska da kuma amfani da barkonon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga zangar da suka yi kokarin kai farmaki kan shelkwatar jam’iyar.

Gwamnati ta kafa dokar hana yawon jiya da dare, a garin da ya kasance tushen zanga zangar da tayi sanadiyar hambare gwamnatin shugaba Zine el Abdidine Ben Ali, da kuma sanadin zanga zanga zangar da ta ratsa kasashen larabawa da kawo sauyi a yankin.

Zanga zanga ta baya bayan nan ta faru ne yayinda jam’iyar kishin Islama Ennnahda ta fara tattaunawa da jam’iyun hamayya da zumar kafa gwamnatin hadin guiwa, kwana guda bayan ta lashe mafiya yawan kuri’u a zaben da aka gudanar irinshi na farko a kasar inda jama’a suka zabi jam’iyar da ransu ke so.

Shugaban jam’iyar Ennahda Rachid Ghannoushi ya yi kira da a kwantar da hankali bisa ga cewarshi, jam’iyarshi zata kafa gwamnati ta hanyar abota da ‘yan’uwantaka.

An fara zanga zangar ne bayan da jami’an zabe suka soke kujerun da jam’iyar hamayya ta Popular List ta samu bisa hujjar sabawa ka’idojin kamfe

XS
SM
MD
LG