Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Shuwagabannin Kasashen Afrika Bai Bar Mata A Baya Ba


Kwararru daga kasashe daban daban na nafiyar Afirka sun fara tattaunawa a birnin Yamai.

Wasu daga cikin muhimman abubuwa da taron kungiyar kasashen Afrika ta 'African Union,' za su mai da hankali akai sun hada da karfafawa kungiyoyin matan shuwagabannin kasashen wannan nahiyar.

Cikin shawarwarin har da fadada ayyukan kungiyar ta OPDAS zuwa OPDAD wato daga yaki da cutar SIDA zuwa wasu fannonin cigaban al’umma.

Tun a watan Fabrairu da ya gabata ne a karshen taron da ta gudanar a birnin Addis Ababa, kungiyar matan shuwagabanin kasashen Afrika OPDAS mai yaki da cutar SIDA, ta ayyana shirin fadada ayyukan ta zuwa wasu fannonin ci gaban al’uma, da nufin karfafa wa gwamnatocin kasashen wannan nahiya gwiwa wajen gudanar da ayyukan ci gaban jama’a.

Dalilin haka ne taron kwararrun dake gudana, da taron kolin kungiyar tarayyar Afrika suka dukufa akan ayyukan tsara ka’idoji da dokokin wannan kungiya dai dai da sabuwar manufar da ta sa a gaba a matsayin ta na sabuwar kungiyar OPDAD.

Madame Mame Ta’a Bossomtwi sakatariyar wannan kungiyar, tace kudurori 6 ke kunshe a fasalin ayyukan da suka bullo da su, ciki kuwa akwai kula da lafiyar mata da yara, magance wariyar da mata ke fuskanta, ci gaban matasa, da kyautata rayuwar al’umma.

Gidauniyar, Guri Vie Meilleure, ita ce ke karbar bakoncin wannan taron, shugabar kungiyar, uwargidan shugaban kasar Nijar Hajiya Aishatou Issouhou, ke farin cikin ganin a Nijar ne ake wannan taron na kungiyar matan shuwagabannin Afrika.

Kungiyoyin kare hakkin mata sun yaba da wannan sabon yunkuri da matan shuwagabannin kasashen Afrika suka yi, sai dai suna yiwa shuwagabanin kungiyar ta OPDAD hannun ka mai sanda.

Hajiya Halima Sarmeye mataimakiyar shugabar kungiyar SOS, tace taron zai yi tasiri amma sai an bar son kai, da kawo siyasa cikin al'amuran kasa.

Bayan tattaunawa da tsawon kwanaki biyu taron kwararun zai gabatar da rahoton sa na taron zuwa jama’a, wanda matan shuwagabannin kasashen Afrika zasu gudanar a ranar 8 ga watan Yuli a birnin Yamai da taron kungiyar tarayyar Afrika.

Ga cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:15 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG