Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tarzoma a Garin Misau Bayan Nadin Sabon Sarki


Tarzoma ya barke a bayan da aka nada sabon sarki Misau, yau da hantsi, tuni dai jami’an tsaro suka shawo kan lamarin, kamar yadda kakakin rundunar ‘yan Sandan jihar Bauchi, DSP, Haruna Muhammad, ya shaidawa wakilin muryar Amurka, Abdulwahab a wata hira .

Shi kuwa Shehu Ahmad, Duba garin Misau, cewa yayi bayan da aka nada Sarki sai tarzoma ta taso amma da yardan Allah, jami’an tsaro sunyi duk abun da ya kamata suyi batare da cutar da kowa ba.

Ya kuma kara da cewa yanzu haka Sarki na cikin Fadar sa kuma Fadar na kewaye da jami’an tsaro gabas da yamma da kudu da arewa.

Da wakilin muryar Amurka, ya tuntubi sabon Sarkin Alhaji Ahamad Suleiman, ya tabbatar masa cewa yana ciin Fada lafiya lau.

XS
SM
MD
LG