Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tashin Bom A Tashar Motar Dukku Garin Gombe.


Panda gigante Xin Xin toma conta de dois filhotes no Jardim Zoológico de Coloane, em Macau.
Panda gigante Xin Xin toma conta de dois filhotes no Jardim Zoológico de Coloane, em Macau.

A garin Gombe bom yatashi a tashar motar dukku kusa da ofishin yan sanda da misalin karfe goma sha daya na safiyar yau.

Hukumar agaji ta red cross ta bada tabbacin akwai mutanen dasuka rasa rayukansu saidai bata bada kididdigarsu ba domin a lokacin da wakilinmu yake hada rahoton suna cikin aikin bada agajine.

Sai dai wata majiya wanda bata hukuma bace ta shaida ma wakilinmu cewa mutane fiye da goma sun mutu.

A tabakin wani mutum dake tashar motar dukku alokacin tashin bom din, yayi bayanin yadda mutane ke watsewa kasancewar rikicewar tashin bom din ga hayaki ya turnuke tashar, shi kansa ya tabbatar da cewa babu yadda za’a iya ganewa mutane nawa ne suka rasa rayukan su.

Ya kuma bayyanawa wakilinmu yadda ake daukar mutane zuwa asibiti, jami’an tsaro dayawa ma na gurin.

Wakilin mu ta wayar salula ya tuntubi sakataren hukumar bada agaji ta red cross a jihar Gombe Abubakar Yakubu, inda yace, “muna aikin agaji muna taimakawa jama’a wanda suka jinkata kuma muna kaisu asibitoci.” Da wakilin mu ya tambayeshi ko zai iya fada mana mutane nawane suka rasa rayukan su, yace tukunna dai har yanzu baza’a iya fada ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG