Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tasirin Hare-haren Jami’an Tsaro Kan ‘Yan Bindiga A Yankunan Sokoto


Yadda ‘Yan Bindiga Ke Karbe Iko Da Kauyuka A Sokoto
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:24 0:00

Yadda ‘Yan Bindiga Ke Karbe Iko Da Kauyuka A Sokoto

A Najeriya, alamu na nuna cewa akwai yiwuwar a samu saukin matsalolin rashin tsaro a wasu yankunan da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga saboda a baya bayan nan ana jimawa ba tare da an kai hari ba a wasu wuraren, sai dai kuma ana fuskantar kananan hare-hare a wasu wurare dabam.

Yanayin rashin tsaro a kasar yana daukar wani salo wanda masu fashin baki ke kallo da fuskoki dabam daban.

Tun lokacin da jami'an tsaron Najeriya suka fara fatattakar ‘yan bindiga a wasu wurare kamar yankin gabashin jihar Sokoto musamman garin Isa, inda aka kona motar wasu matafiya har suka mutu, mazauna yankunan sun ce ana samun saukin hare-haren ‘yan bindiga, kamar yadda masanin al’amuran yau da kullum Bashir Altine Guyawa ya bayyana.

Shi ma wani mazaunin yankin da ya so a sakaya sunansa, ya ce akwai saukin hare-haren amma kuma akwai wani ‘dan bindiga da har yanzu ya ke addabar wasu yankunan garin na Isa.

A garin Illela dake gabashin Sokoto, mazauna yankin sun ce akwai alamun ‘yan bindigar da ake fatattaka a yankin Isa sun soma kwararawa wani daji dake tsakanin garin Illela da Gwadabawa.

Detective Auwal Bala Durumin Iya, shugaban sashen nazarin aikata laifuka da tsaro a jami'ar Yusuf Maitama Sule dake Kano, ya ce sakin wasu mutane da shahararren dan bindiga Bello Turji ya yi, wata dabara ce ta neman afuwa daga gwamnatin tarayya domin ya ga an takura mashi.

Dama dai masana sun jima suna bayar da shawarwari akan cewa idan za'a murkushe ‘yan bindiga to a tunkaresu gaba daya, domin gudun kada wasunsu su yi kaura zuwa wani wuri su ci gaba da aikata ta'asa.

Saurari rahoton Muhammadu Nasir cikin sauti:

Mazauna Wasu Yankunan Jihar Sakkwato Sun Ce Sun Fara Ganin Saukin Hare-Haren ‘Yan Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00


XS
SM
MD
LG