Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tattauna Matsalar Najeriya a Amurka


Jihar Iowa, mai sanyin gaske a lokacin dari.

​A karshen makon wannan wata na Afrilu ne ake gudanar da wani taro a Jami’ar Grand View dake jihar Iowa a nan Amurka domin tattauna matsalar tsaro da neman wa Najeriya zaman lafiya.

Sashen Hausa na Muryar Amurka ya tuntubi daya daga cikin jami’an da suka shirya taron, Farfesa Ahmadu Baba-Singhri, dan asalin Jihar Bauci domin jin ko mene ne yasa suka shirya taron.

“Abunda yasa na shirya wannan taro, shine abubuwan dake faruwa a Najeriya. Ni dan Najeriya ne, saboda haka abun yakan dame mu sosai,” a cewar Farfesa Singhri.

Mr. Baba-Singhri ya cigaba da cewa “Shine muka ce, yadda za’a taimaka shine mu kira mutane manyanmu, suzo mu tattauna a samu hanyar da za’a cimma zaman lafiya a kasarmu”.

Daga cikin wadanda suke hallartar taron akwai gwamnan Jihar Bauci Isa Yuguda, da babban alkalin jihar Justis Ibrahim Zango, da alkalin alkalan kotun shar’ia Abdullahi Marafa da kwamishinoni da wasu shuwgabanni.

Za’a kwashe kwanaki 6 ana gudanar da wannan taro, wadanda yawancin wadanda ke hallartarsa daga Jihar Bauci suke.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:50 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG