Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamna Dankwambo Ya Kare Jonathan


Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo
Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo

A kokari da shuwagabanni a Najeriya suke yi na gani zaman lafiya ya dawo yankin arewa maso gabashin kasar, gwamnan jihar Gombe Ibrahim Hassan Dankwambo ya fadi irin tanadin da shugaba Jonathan yakewa wannan yanki.

A hirar da yayi da Aliyu Mustaphan Sokoto na sashen Hausa, Gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo ya bayyana cewa shi da ragowar gwamnoni biyar dake wannan yanki (Borno, Adamawa, Bauci, Yobe da Taraba) sun yi taro domin shata shirin da suke gani zai kawo wa wannan yanki walwala da zaman lafiya.

Mr. Dankwambo yace “maigirma shugaban kasa, ya bamu tabbacin cewa idan aka gama, aka fidda ‘fasalin cigaba’, aka kai masa, zai saka a cikin tsarin kudi”.

Game da batun korafin da jama’a suke yi na cewa shugaban yaki zuwa jihohin arewa maso gabas, gwamna Dankwambo cewa yayi “shugaban kasa mutum ne mai abubuwa mai abubuwa da yawa, da kuma wahala kwarai da gaske. Kuma idan babu dalili ban ga abunda zai kaishi wurare da dama ba, kamar yadda ake fada.”

Gwamna Dankwambo ya rufe da cewa, kamar yadda yake ji, shugaba Jonathan zai dauki lokaci ya zagaye jihohin dake fama da matsaloli a arewacin Najeriya.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG