Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tazarar Haihuwa Karin Lafiya Ne Ga Iyaye Mata Da 'Ya'yansu


Babbar asibitin dake Damagaram a jamhuriyar Nijar, ya shirya wani babban taron na mata domin fadakar da su kan tazarar haihuwa.

Wata jami’ar asibiti dake Damagaram ta fadakar da mata game da riga kafin sankarar mahaifa, da cutar Sida da kuma bada tazara tsakanin haihuwa.

Dr, Jakite, mai duba mata a babbar asibitin Damagaram, tace ganin yadda matsalar take Kamari shine dalilin fadakar da matan, akan tazarar haihuwa domin a cewar ta hakkan nada mahimmanci domin yana rage mace macen yara kanana da iyaye mata.

Ta kara da cewa gwamnati ta kara masu karfin gwiwa da samarda magunguna domin a taimakawa mata da maza da kuma yara kanana domin su kasance masu koshin lafiya. Ta kuma ce akwai bincike na sankarar mahaifa da na HIV ko SIDA wanda take karfafawa mata gwiwar su tabbatar da cewa sunyi wannan bincike wanda za’ayi masu shi cikin zuri .

Suma matan da suka halarci taron sun nuna kamsuwarsu ga tasiri fadakarwar ga lafiyarsu dana ‘ya’yansu, wasu kuma sun bada shawarar cewa zuwa asibiti karbar maganin tazarar haihuwa baya likita ya gwada mace shine yafi dacewa ba sayansa a katin magani ba.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:09 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG