Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Theresa May Ta Gana Da Donald Trump A Fadar White House


Fira ministan Birtaniya Theresa May, ta gana da Shugaban kasar Amurka Donald Trump a yau Juma’a a fadar White House, inda shuwagabannin biyu suka amsa tambayoyi ga ‘yan jarida.

Theresa May itace shugabar wata kasa ta farko da ta gana da Trump a Washington tun da ya dare kan ragamar mulki.

Dukansu biyun sun dauki matakan yiwa dangantakar su da wasu kasashe kwaskwarima musamman akan harkokin kasuwanci.Shirin ficewar Birtaniya daga kungiyar tarayyar turai da kuma fitar da Amirka daga kungiyar kasuwanci kasashen 12 ta Pacific da shugaba Trump yayi, ya zama wajibi suyi shawarwari kula sabbin yarjejeniyoyin harkokin kasuwanci a fadin duniya baki daya.

Tsarin da Teresa May take dashi na fitar da kasar ta daga kungiyar tarayyar Turai ya hada da bada muhimmanci akan iko kan shige da ficen baki, duk da dai har yanzu bata bayyana hakikanin tsarin dokar ba.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG