Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Thomas ta Zama Daya a Cikin Wutar Daji Mafi Muni a Tarihin California


Wutar Daji a California
Wutar Daji a California

Jami’an kasshe gobara a jihar California dake yammacin Amurka sun maida hankali wurin kashe wutar daji da ta tashi a Arewa maso Yammacin Los Angeles wanda ta riga ta zama daya a cikin wautar daji da suka fi yin barna a tarihin jihar.


Wutar daji da aka mata lakabi da Thomas ta kona fillayen daji da ya kai kilomita 930 kana ta lalata gine gine 800 a karamar hukumar Santa Barabara tun lokacin da ta fara a makon da ya gabata. Hukumomi sun ce kashi goma na harshen wutar ce aka kashe, kuma a yayin da masu kashe gobarar ke samun nasara ta sama, wutar na ci gaba da zama mai hadari da zata iya yaduwa cikin gaggawa ta iska.


Jami’ai dari bakwai da hamsin ne suke aikin kashe wutar da ake kira Thomas, wacce ta fi ci a kudnacin California.


Wutar ta tilasta kwashe mutane dubu dari biyu daga gidajensu. Adadin mutane ya karu ne a shekaranjiya Lahadi yayin da aka kwashe mutane masu yawa a Santa Barbara, a lokacin da wannan gagarumar wuta take kara bazuwa a yankin.


Shugaba Donald Trump ya dau mataki a ranar Juma’a a kan wutar, inda ya ayyana dokar ta baci ta tarayya a Califonia, wanda ya baiwa hukumomin tarayya daman shirya kai dauki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG