Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Bukaci Ma’aikatun Gwamnati Su Fitar Da Rahoton Kasafin Kudi Duk Wata


Shugaba Bola Ahmed Tinubu (Facebook/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu)
Shugaba Bola Ahmed Tinubu (Facebook/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu)

A wani  yunkuri na tabbatar da tsarin kasafin kudi mai inganci, Shugaba Bola Tinubu ya umurci dukkanin ma’aikatu da hukumomin gwamnati su rika fitar da rahoto duk wata kan yadda suka aiwatar da kasafin kudin 2024.

ABUJA, NIGERIA - Da yake jawabi a wurin rattaba hannun a fadar shugaban kasa da ke Abuja, Shugaba Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa, gwamnati zata rinka bibiyar aiwatar da kasafin kudin na Naira tiriliyan 28.7 cikin tsanaki tare da sanya ido a kai.

Ya zayyana muhimman matakan da za a bi don tabbatar da bin ka’ida da inganci wajen aiwatar da kasafin kudin.

"An umurci dukkanin hukumomi da ma’aikatun gwamnati su sani cewa, suna da nauyi da ya rataya akan su na bayar da rahoton ayyukan kasafin kudi wata-wata ga ma'aikatar kasafin kudi da tsare-tsare ta tattalin arziki, wanda kuma zai tabbatar da sahihancin hakan." Inji shugaba Tinubu.

Tinubu ya gabatar da kasafin kudin 2024 a gaban majalisa
Tinubu ya gabatar da kasafin kudin 2024 a gaban majalisa

Don kara inganta sa ido tabbatar da tabbatar da nasarar aikin, Shugaban kasar ya sanar da cewa, Ministan Kudi da na Tattalin Arziki za su rika yin bita akai-akai . Bugu da kari, Shugaba Tinubu ya tabbatar da aniyarsa ta ganin nasarar tsarin ta hanyar jagorantar tarukan Majalisar hadin kan tattalin arziki lokaci-lokaci.

Kasafin kudin shekarar 2024 mai taken 'kasafin kudin sabunta fata' ya ware kudade ga muhimman fannonin da za a fi ba da fifiko, da suka hada da tsaron cikin gida, samar da ayyukan yi, daidaita tattalin arzikin kasa, ingantaccen yanayin saka hannun jari, bunkasa jari, rage talauci, da samar da zaman lafiya.

Sabbin kudin Naira
Sabbin kudin Naira

Shugaban ya karkare da yin gargadi ga ma’aikatu da hukumomin gwamnati yana mai cewa, “Ina so in tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa, an gargadi dukkan hukumomi da ma’aikatun mu da cewa, idan baza su iya aiwatatar da ayyukan gwamnati bisa inganci, sadaukarwa da amana ba, to lallai ya fi masu su tafi su bar aikin mu muyi a madadin su”

A hirar shi da Muryar Amurka dangane da batun, Yusha’u Aliyu kwararran mai sharhi kan tattalin arziki,yace, dole a yaba wa Shugaba Tinubu da daukar wannan matakin da aka dade ana kira gwamnati ta dauka, da irin tsarin da ya kawo wajen ganin ana duba ayyukan ma’aikatu da jami’an gwamnati a kowanne wata tare da samar da rahotanni.

Haka zalika, yace, Majalisa kanta ta ambaci cewa, zata rika sa ido kan abubuwa irin wannan saboda tabbatar da nasarar shirin da kauda duk wata badakala.

Aliyu, yace babu shakka irin wadannan matakai zasu habbaka arziki da gina tattalin arzikin kasa.

Shugaba Tinubu (Hoto: Facebook/Bola Tinubu)
Shugaba Tinubu (Hoto: Facebook/Bola Tinubu)

A yayinda gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta dauki wadannan matakai na ganin an samar da yanayi na gaskiya da rikon amana a ma’aikatun gwamnati, mafi akasarin masu sharhi kan al’amuran yau da kullum sun yi maraba da irin wadannan matakai, yayinda ake cigaba da sa’ido zuwa wani lokacin don ganin yadda hukumomi da kwamitocin da aka dorawa alhakin bin diddigin ayyukan na ma’aikatun gwamnati zasu aiwatar da ayyukansu bisa gaskiya da rikon amana.

-Yusuf Aminu Yusuf~

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG