Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ba Shi Da Niyyar Korar Robert Mueller - Fadar White House


Robert Mueller
Robert Mueller

Fadar gwamnatin Amurka ta White House ta ce ba ta da wani shiri na sallamar shugaban kwamiti na musamman da ke binciken zargin shisshigin da Rasha ta yi a zaben Amurka na 2016.

Wani babban Lauya a Fadar shugaban Amurka ta White House, ya ce shugaba Donald Trump ba shi da niyyar koran Robert Mueller, shugaban da ke jagorantar kwamitin da ke bincike kan zargin katsalandan din Rasha a zaben Amurka.

Kalaman lauya Ty Cobb na zuwa ne, duk da korafe-korafen da shi Trump ya yi a shafinsa na Twitter, inda yake zargin jami’in da cewa yana cusa son rai na siyasa a binciken da yake gudanarwa.

Cobb, ya ce duk da maganganun da hasashen da kafofin yada labarai suka sha yi kan wannan lamari, Fadar White House ba ta da wani kuduri na ganin bayan Mueller.

Trump dai ya zargi Mueller da cewa yana nuna son rai na siyasa a binciken da yake gudanarwa na kokarin gano alakar Rasha da zaben da aka yi a Amurka a shekarar 2016.

Kwamitin na Meuller har ila yau, yana kokarin ya gano ko akwai wani yunkuri da shi shugaba Trump ya yi na kawo cikas a cikin yadda ake tafiyar da binciken.

Trump ya ce yana mamakin “ko me ya sa Mueller ke da rikakkun ‘yan jam’iyyar Democrats 13 a kwamitin da kuma wasu masu goyon bayan Hillary, amma kuma babu dan jam’iyyar Republican ko daya a cikin ‘yan kwamitin binciken na sa?”

Sai dai kuma rahottani sun nuna cewa Trump ya kasa lura da cewa hatta shi kansa Mueller din ya yi rajista ne a matsayin dan jam’iyyar Republican.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG