Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

"Trump Bai Ba Da Umurnin a Janye Dakarun Amurka Daga Afghanistan Ba"

Mukaddashin Sakataren Tsaron Amurka, Patrick Shanahan
Mukaddashin Sakataren Tsaron Amurka, Patrick Shanahan

“Ban samu umurnin rage yawan sojojinmu da ke Afghanistan ba,” abin da Shanahan ya gaya ma manema labarai kenan, gabanin ziyarar ba-zata da ya kai birnin Kabul jiya Litini.

Mukaddashin Sakataren Tsaron Amurka, Patrick Shanahan, ya ce bai samu umurni daga Shugaba Donald Trump na janye sojojin Amurkan daga Afghanistan ba.

“Ban samu umurnin rage yawan sojojinmu da ke Afghanistan ba,” abin da Shanahan ya gaya ma manema labarai kenan, gabanin ziyarar ba-zata da ya kai birnin Kabul jiya Litini.

Ya kara da cewa, “umurnin da aka bayar, tare da hadin gwiwar Sakataren harkokin waje, Mike Pompeo da mai bayar da shawara kan harkokin tsaron kasa, John Bolton, shi ne a goyi bayan jakada na musamman Zalmay Khalilzad wajen tattaunawar cimma zaman lafiya.”

Makon jiya, a yayin jawabi ma Amurkawa kan makomar kasar, Trump ya sake yin tir da dadaddun fitintinun da ake fama da su- kama daga Syria zuwa Afghanistan - yana mai cewa “manyan kasashe ba su yaki har abada.”

Ya gaya ma taron jama’a cewa yayin da jami’an diflomasiyyar Amurka ke samun ci gaba a tattaunawar samar da zaman lafiya a Afghanistan, “za mu iya rage yawan sojojinmu a kasashen waje, mu samu mu maida hankali kan hanyoyin dakile ta’addanci.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG