Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taliban Sun Hallaka Dakarun Afghanistan 40


Zaman tattaunawa tsakanin jami'an Afghanistan da 'yan kungiyar Taliban.

Rahotanni na nuni da cewa ranar Talata mayakan kungiyar Taliban suka kashe dakarun Afghanistan.

Yan Ta'addan Taliban sun kashe dakarun gwamnati 40 a wasu hare-hare da suka kai arewa maso gabashin Afghanistan a daidai lokacin da ake ci gaba da wani taron sulhu a birnin Moscow na kasar Rasha domin kawo karshen rikicin.

Farmaki mafi muni da yan ta’addar suka kai da safiyar Talata shine wanda suka kai kusa da babban birnin Kunduz, a cewar jami’ai da mazauna yankin.

Saifullah Amiri, Mataimakin shugaban gundumar ya fadawa kafofin watsa labaran Afghanistan cewa mayakan Taliban sun hallaka sojoji 22 da ‘yan sanda 3, yayinda aka raunata wasu 20.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG