Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump: Bani Ne Sanadin Da Turkiyya Ta Mamaye Arewacin Siriya Ba


Shugaban Amurka ya ce baya so ya shiga cikin yakin da ake yi tsakanin Trukiyya da Siriya.

Shugaban Amurka, Donald Trump, na ci gaba da musanta zarginsa da ake cewa, shi ne sanadin da Turkiyya ta mamaye arewacin Siriya.

Trump ya musanta zargin ne a wani taron manema labarai da ya yi a jiya Laraba, a lokacin da wani dan jarida ya tambaye shi ko ganawar da suka yi ta yi da takwaran aikinsa Recep Tayyip Erdogan ne ta kai ga mamayar da Turkiyyan ta yi wa arewacin Siriya.

Hakan kuma na faruwa ne a daidai lokacin da shugaban na Turkiyya ke shirin ganawa da mataimakin shugaban Amurka Mike Pence, da Sakataren harkokin wajen kasar Mike Pompeo a yau Alhamis.

A baya, rahotanni sun ruwaito Erdogan yana cewa da Shugaba Trump kadai zai gana idan ya je Turkiyyan, kalaman da aka fassara su a matsayin “ba zai gana da manyan jami’an gwamnatin Amurkan ba,” amma kuma ga dukkan alamu ya sauya matsayarsa.

Shugaban Turkiyyan ya ce, “ba zan tattauna da kowa ba illa Pence da Pompeo.”

Facebook Forum

Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

An Ga Watan Azumi A Najeriya - Sultan

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammada Sa'ad Abubakar Ya Ba Da Sanrwar Ganin Watan Ramadan
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

An Kai Wa Ofisoshin Kungiyar Ba Da Agaji Hari A Arewa Maso Gabashin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:02 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG