Kwana daya, bayan da wasu hotuna dake nuna yanayin tashin hankalin, da ake ciki a wasu cibiyoyin tsare bakin haure guda biyu a jihar Texas suka bayyana a yanar gizo, shugaban Amurka Donald Trump ya ce, in da yawancin bakin hauren su ke yanzu, ya fi masu akan in da suka fito.
“Idan har bakin hauren, ba sa jin dadin yanayin da suke ciki a cibiyoyin da aka gina masu, to kawai ku fada masu, kada su zo kasar mu, abinda Trump ya rubuta kenan a shafin sa na yanar gizo jiya Laraba. Ya kara da cewa “kun ga an warware duk wata matsala."
Trump ya dora laifin matsalar bakin hauren akan abunda ya kira “dokokin shige-da-fice na ‘yan jam'iyyar Democrats.”
“Mutane ne wadannan sun zo Amurka, don nemawa kansu rayuwa mai kyau, abinda Sanata Chuck Schumer, jigo a jam’iyyar Democrat, ya rubuta ke nan a twitter, a matsayin maida martini ga rubuce-rubucen Trump. Ya kara da cewa, lokaci yayi da ya kamata shugaban ya tuna da abubuwan da Amurka ke karewa.
Za ku iya son wannan ma
-
Fabrairu 23, 2021
Jirgin Hukumar Sama Jannatin Amurka Ya Isa Tashar Sararin Sama
-
Fabrairu 22, 2021
COVID-19 :Adadin Wadanda Suka Mutu Ya Kusa Rabin Miliyan A Amurka
-
Fabrairu 20, 2021
Amurka Ta sake Komawa Cikin Yarjejeniyar Sauyin Yanayi A Hukumance
-
Fabrairu 17, 2021
Texas-Dussar Kankara Ta Haifar Da Dauke Wuta A Gabashin Amurka
-
Fabrairu 14, 2021
Yadda Majalisar Dattawan Amurka Ta Wanke Trump
Facebook Forum