Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Na Cigaba Da Kare Shiga Tsakani Kan Shari'ar Wani Sojan Ruwan Amurka


Donald Trump
Donald Trump

A jiya Litinin shugaban Amurka Donald Trump ya sake bada wani jawabi da ya saba da abinda aka yi na yin canji a shugabancin a ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon.

Trump ya yi jawabin ne yayin da yake kare matakin da ya dauka a madadin wani sojan ruwan Amurka da aka yankewa hukunci na aikata ba daidai ba a lokacin yaki da kungiyar ‘yan ta’adda ta IS a Iraqi.

A lokacin da aka tambaye shi akan korar Sakataran Sojojin Ruwan Amurka ranar Lahadi wanda farar hula ne, Richard Spencer, Trump ya fadawa manema labarai a farar White House cewa, “Mun jima muna tunanin daukan wannan mataki.”

“Amma hakan bata faru ba,” sannan a lokacin da ya bayyana a ofishin na shugaban kasa tare da Firaiministan Bulgaria ya kara da cewa, “Dole na kare mayakan da suka yi yaki.”

Shugaba Trump ya kuma kare umarnin da ya bawa Sakataran Tsaron Amurka, Mark Esper, a ranar Lahadi da ta gabata da ya soke shawarwarin da hukumar daraktoci da ta saurari karar akan Chief Petty Officer Edward Gallagher.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG