Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Na Ganawa Da Juncker A Kan Cinikayyar Amurka Da Turai


Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban Hukumar Zataswar Kungiyar Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker
Shugaban Amurka Donald Trump da Shugaban Hukumar Zataswar Kungiyar Tarayyar Turai Jean-Claude Juncker

Batun haraji shine kan gaba a tattaunawa da shugaban Amurka Donald Trump zai yi da shugaban zartarwar kungiyar Taryyar Turai Jean-Claude Juncker a yau Laraba.

Juncker zai shigo nan Washington ne da tunanin Kungiyar Tarayyar Turai zata kaucewa rikicin cinikayya ta hanyar fahimtar da Trump ya janye haraji masu tsauri da yake niyar dorawa motocin Turai. Wannan harajin motoci zai addabi masana’anatar kera motoci ta kasar Jamus da take samun habbaka, sai kuma batun harajin nan da Trump ya riga ya doawa dalama da karafe.

Amma kafin ganawar ta su, Trump yace yana kyautata zaton bangarorin biyu zasu cimma wata yarjejeniya, biyo bayan barazanan da shugaban na Amurka ya yi cewa zai yi karin haraji a kan abokan cinikayyar Amurka.

Da safiyar jiya Talata shugaban Amurka yace “haraji muhimmin abu ne, kana kuma ya yi barazanar yin karin haraji a kan abokan kasuwancin Amurka.

Hukumar zartarwar kungiyar Tarayyara Turai ta mayar da martani a kan harajin da Amurka ta dorawa kayanta, amma kuma harajin da za a dorawa motoci zai sa Turai kara daukar sabbin matakai.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG