Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump na Shirin Sanar da Sabon Mataki a Kan Yarjejeniya Nukiliyar Iran


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaba Donald na shirin sanar da sabon mataki da gwamnatinsa zata dauka a yarjejeniyar shirin nukliyar Iran ta shekarar 2015 wanda Amurka da tabbatar da shi karkashin shugabancin tsohon shugaba Barack Obama.

Biyo bayan kiraye kiraye da kawayen Amurka na kud da kud da wasu jami’an gwamnatinsa , akwai alamar shugaban Amurka Donald Trump zai yi watsi da kirar a yau Juma’a ya dakatar yarjejeniyar shekaru biyu da aka kulla a kan shirin makaman nukiliyar Iran kuma ya ci gaba da bayyan sabon mataki da zai dauka a kan Tehran

Da sanyi safiyar yau Juma’a, fadar White House ta bada sanarwar cewa, bayan shawara da tawagar tsaron kasar, ta amince da wani sabon tsarin a kan Iran.

Wakilan majalisar dokoki sun ce tun da yake Trump ba zai aminta da wannan yarjejeniya da aka kira da shirin hadin gwiwa mai inganci, toh kuma ba zai nemi Majalisun su yi Karin wani takunkumi a kan Iran ba.

Shugaba Trump yana nuna tsananin ga wannan yarjejeniya amma babu wani kwakkwarar mataki da yake dauka na sokewa ko barin shirin, inji wani wakilin majalisar dattawa na Democrat kuma mamba na kwamitin huldar kasashen waje Sanata Chris Coon yaka fadawa talbijin MSNBC.

Tun shekarar 2015 da wakilai biyar na Iran na dindindin kwamitin sulhun MDD da Kungiyar tarayyar Turai suka tabbatar da wannan yarjejeniya, Trump yake adawa ga wannan nshirin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG