Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Na Yunkurin Soke Shirin Tambolar Shiga Amurka Ta “Lottery”


A lokacin da shugaba Donald Trump yake bayyana shirinsa na gabatar da kudurin dokar rage adadin bakin da ke shiga Amurka

Shugaban Amurka Donald Trump na kokarin soke shirin tambola na "Lottery" da kuma tsaurara matakan samun katin zama a kasar na dindindin wato Green Card, a wani kudurin dokar da yake so ya gabatarwa majalisar dokokin kasar.

Shugaban Amurka Donald Trump, na kokarin bayyana wani kudurin doka da zai rage adadin mutanen da ke shiga kasar bisa ka’ida, tare da hadin kan wasu sanatoci ‘yan jam’iyar Republican biyu da suka tattauna da shugaban a Fadar White House.

A farkon shekarar nan, Sanata Tom Cotton da David Perdue suka gabatar da wata doka da za ta rage adadin bakin da ke shiga kasar daga miliyan daya zuwa dubu 500 a kowace shekara.

Kudirin har ila yau, zai nemi rage adadin ‘yan uwan bakin da ke shiga kasar, da kawo karshen shirin tambola na lottery da kuma tsaurara matakan samun katin zama a Amurka na dindindin, wato Green Card.

Sau biyu Trump yana ganawa da sanatocin kan wannan kudirin dokar, wanda yunkuri ne na cika daya daga cikin alkawuran da ya yi na kawo sauyi a fannin shige da ficen kasar.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG