Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Bukaci Israila Ta Dakatar da Gine-gine A Yankin Falasdinawa


Firayim Ministan Israila Netanyahu a hagu da Shugaban Amurka Donald Trump a dama
Firayim Ministan Israila Netanyahu a hagu da Shugaban Amurka Donald Trump a dama

Shugaban Amurka Donald Trump da Firayim Ministan Isira'ila Benjamin Netanyahu sun jaddada muhimmancin zaman lafiya a ganawar da suka yi a Fadar White House jiya Laraba, duk da cewa Trump ya nuna cewa zai yi na'am da duk wata sabuwar hanyar warware rikicin na Isira'ila da Falasdinu, koda kuwa ba ta hada da kafa kasashe biyu ba.

Bayanin Trump na cewa Amurka na iya yin na'am da tabbatar da kasancewar kasa daya tilo a yankin, a matsayin mafita mai dorewa, al'amarin da ka iya gurgunta kokarin da Amurka ta shafe shekaru da dama tana yi, na ganin an kafa kasar Falasdinu da zata yi makwaftaka da Isira'ila.

"Ina nazarin batun kafa kasashe biyu wuri guda da kuma batun tabbatar da kasa daya tilo, amma zabin da bangarorin biyu su ka fi so, shi ni ma na fi so," a cewar Trump a yayin wata hira da manema labarai ta hadin gwuiwa da Netanyahu. Ya kara da cewa, "Zan iya harka da kowane zabi. Da na ga kamar kafa kasashe biyu zai fi, to amma fa a kashin gaskiya, muddun Isira'ila da Falasdinu su ka kasance cikin farin ciki, to ni ma zan yi farin ciki da zabin da su ka yi."

Yayin taron manema labaran, Trump ya kuma bukaci Netanyahu da ya "dan dakatar" da aikin fadada matsugunan Yahudawa a yankunan da Isira'ila ta mamaye, yayin da Fadar White House ke kokarin farfado da batun cimma zaman lafiya a Gabas Ta Tsakiya.

XS
SM
MD
LG