Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Caccaki 'Yan Majalisar Dokoki Kan Bincikensa


Shugaba Trump a lokacijn taron CPAC 2019, a Oxon Hill, Md., ranar 2 Maris, 2019.
Shugaba Trump a lokacijn taron CPAC 2019, a Oxon Hill, Md., ranar 2 Maris, 2019.

A lokacin da yake jawabi a taron, shugaba Trump ya zargi shugaban kwamitin tattara bayanan sirri mai dauke da ‘yan Democrat, Adam Schiff da wasu ‘yan majalisar da bai ambaci sunayensu ba.

Shugaban Amurka Donald Trump, ya gabatar da wani jawabi a taron shekara-shekara da ake yi, wanda ke tattaro masu ra’ayin siyasar mazan jiya.

Taron ya biyo bayan ganawarsa da shugaban Korea ta Arewa Kim Jong Un, wacce ba ta yi nasara ba, da kuma kazamar shaidar da tsohon lauyansa, Michael Cohen ya bayar a gaban majalisar dokokin Amurka.

Kamar dai yadda wasu suka yi tsammani, taron ya zamanto wata kafa da ta dauke hankalin shugaba Trump daga kacaniyar abubuwan da suka faru a makon da ya shude, yayin da ake ganin alamar cewa, binciken da kwamitin Robert Mueller ke yi kan zargin hadin kai, tsakanin kwamitin yakin neman zaben Trump da Rasha, ya kusa kawowa karshe.

A lokacin da yake jawabi a taron, shugaba Trump ya zargi shugaban kwamitin tattara bayanan sirri mai dauke da ‘yan Democrat, Adam Schiff da wasu ‘yan majalisar da bai ambaci sunayensu ba, da laifin mayar da hankali daga binciken na kwamitin Mueller, zuwa kan harkokin da suka shafi kudadensa.

Taron na masu ra’ayin siyasar mazan jiyan, ya yabawa Trump kan matakan da yake dauka domin hana shiga kasar ta barauniyar hanya, da kuma nada Alkalan kotu masu ra’ayin mazan jiya.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG