Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Ce Ba Ya Tunanin Yi Wa Manafort Afuwa

Paul Manafort
Paul Manafort

An same shi ne da laifin hada wata makarkashiyar jirkita tunanin shaida, a bincikensa da aka yi masa kan ayyukan da ya yi wa tsohon shugaban Ukraine mai goyon bayan shugaban Rasha aka samu Manafort da laifi.

Shugaba Trump ya ce, ba ya jin dadi, dangane da abin da ke faruwa da tsohon shugaban kwamitin yakin neman zabensa Paul Manafort, amma ya ce, ba ya tunanin yi masa afuwa.

Wata kotu a nan Washington, ta yanke wa Manafort hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru 3.5 a jiya Laraba.

An same shi ne da laifin hada wata makarkashiyar jirkita tunanin shaida, a bincikensa da aka yi masa kan ayyukan da ya yi wa tsohon shugaban Ukraine mai goyon bayan shugaban Rasha aka samu Manafort da laifi.

Wannan hukunci na Manafort na zuwa ne, bayan wani hukuncin na daban da aka yanke masa na tsawon kusan shekaru hudu kan badakalar haraji.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG