Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Numberg Tsohon Hadimin Trump Ba Zai Hada Kai Da Mai Bincike Na Musamman Ba


Robert Mueller mai binciken na musamman akan zargin katsalandan da aka ce Rasha ta yiwa zaben shugaban kasar Amurka na shekarar 2016

Sam Numberg tsohon hadimin Shugaba Trump ya shaidawa gidan talibijan na MSNBC ba zai hada kai da binciken zaben 2016 da Robert Mueller ke yi ba

Wani tsohon hadimin shugaban Amurka Donald Trump yace ba zai bada hadin kai a gayyatar da aka yi masa ya bayyana gaban kwamitin dake binciken katsalandar da ake zargin Rasha da yi a zaben shugaban kasa na shekara ta dubu biyu da goma sha shida ba.

Sam Nunberg ya shaidawa tashar MSNBC cewa, “ba zan bada hadin kai ba, “menene zai sa in shafe sa’oi tamanin ina binciken wasikun email da nayi musanyarsu da wasu?

A hirarraki dabam dabam da yayi da kafofin watsa labarai jiya Litinin da rana, Numberg ya bayyana binciken a matsayin bita da kulli, ya kuma ce ba yana kin bada hadin kai bane da nufin kare shugaba Trump.

Ya shaidawa tashar MSNBC cewa, “bari muga abinda Mr. Mueller zai yi. Ina jin zai zama abin dariya idan ya kama ni.” Ina jin zai zama abin dariya matuka idan suka nemi su kama ni”.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG