Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Ce Yan Dimokarat Masu Son Bincikensa Sun Tabu


Shugaban Amurka Donald Trump

Trump ya shiga nuna matukar bacin ransa game da takardun neman bayanai da kwamitin shari'a na majalisar wakilai karkashin Jerrold Nadler su ka aika ga wasu makusantansa da zummar bincikensa.

Shugaban Amurka Donald Trump ya caccaki ‘yan jam’iyyar Dimokarat jiya Talata, saboda kaddamar da jerin bincike da su ka yi kansa da kuma gwamnatinsa, ya na mai bayyana hakan da “wani babban lalube da zummar samo laifi.”

Ya ce ‘yan Dimokarat da ke Majalisar Wakilai, wadanda a ranar Litini su ka bukaci takardun bayanai daga kafofi 81 da su ka hada da mutane da kuma kamfanoni masu nasaba da yakin neman zaben 2016, da harkokin kasuwancinsa da kuma wa’adin tsawon shekaru biyu da ya yi, a ta bakinsa, “sun tabu.” Ya ce an aika da wasikun neman bayanai ma “mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba don kawai a tozarta su.”

A wani rubutu da ya yi ta kafar twitter, Trump ya bayyana binciken da kwamitin Majalisar Wakilai kan Shari’a da, abin da ya kira, “wuce gona da iri, mafi tsanani da aka taba yi a tarihin kasarmu. ‘Yan Dimokarat na yin karan tsaya ga harkar shari’a, kuma ba su son a yi aikin komai.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG