Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Dakatar Da Batun Korar Bakin Haure


Donald Trump
Donald Trump

A wani mataki mai al’ajabi, shugaban Amurka Donald Trump yace ya dakatar da batun aikin korar dubban bakin hauren da basu da takardun zaman Amurka da jami’an hukumar shige da fice zasu fara a yau Lahadi, har sai ‘yan makwanni masu zuwa.

Bisa da roko da ‘yan Democrats suka yi, na jinkirtar da batun korar bakin hauren da basu da izinin zuwa makwanni biyu masu zuwa, domin gani ko Democrats da Republican zasu yi aiki tare a kan magance batun karbar masu neman mafaka da kuma matsalolin kan iyakar kudancin kasar, inji Trump a wani sakon Twitter da ya fitar jiya Asabar da rana.

Rohatanni a kan shirin da hukumar fice da shige tayi na aiwatar da aikin korar dubun dubatar bakin haure, sun tada hankali wasu shugabannin jami’iyar Democrats a manyan birane da dama kana sun yi Allah wadai kuma suka tashi haikan domin taimakawa wadanda abin zai shafa.

Kakakin majalisar wakilai Nancy Pelosi tayi magana da shugaban kasa da yammacin ranar Juma’a inda ta nemi ya jinkirta aikin korar, a cewar kamfanin dillancin labaran Associated Press.

Pelosi ta bukaci ya fasa korar bakin haure kwata kwata. Ta kuma fitar da wata sanarwa a jiya Asabar tana kira ga Trump tun kafin ya sanar a sakon twitter cewa ya jinkirta aikin kamen bakin hauren, inda ta kuma roki shugaban kasar da ya nuna irin tausayawa da ya yi a ranar Juma’a a lokacin da ya fasa kai hari a kan kasar Iran.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG