Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Kara Hasashen Sa Na Adadin Mutane Da Zasu Mutu Sanadiyyar COVID-19


Shugaban Amurka Donald Trump ya kara a hasashensa na adadin mutane da zasu mutu sanadiyyar annobar COVID-19, a yayin da yake alkawarin karin tallafin tattalin arziki, a daidai lokacin da yake nazarin yiwuwar kara bude al’ammura a kasar.

“Zamu iya rasa mutane da za su kai dubu 75, 80 har zuwa dubu 100. Wannan munmunan abu ne, Trump ya fada a yayin wata ganawar da gidan talabijin na Fox News suka yi da shi a daren jiya Lahadi.”

A makon da ya gabata ya ce hasashe na bayyana cewa, kimanin mutane dubu 60 zuwa dubu 70 ne zasu mutu sanadiyyar cutar ta coronavirus.

A dai-dai lokacin da Majalisar dattawan kasar ke shirin komawa bakin aiki a yau Litinin, Trump ya ce gwamnatin tarayya na iya rubanya kudin da ta ware na taimakon gaggawa daga biliyan $3. Ya zuwa yanzu kudaden tallafin sun kai ga taimakawa ‘yan kasuwa masu kananan karfi, wanda zasu iya ci gaba da kasuwancin su, da samar da kayan aiki a asibitoci da kuma baiwa ‘yan kasa kudade. A cewar Trump “karin taimako na kan hanya”

Shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa Mitch McConnell ya ce, zauren majalisar su zasu koma bakin aiki don ci gaba da daukar matakan yaki da annobar COVID-19, da ma wasu ayyukan gaggawa.

“A baki dayan kasar Amurka, ma’aikata na daukar shawarwarin jami’an kiwon lafiya, na daukar matakan da suka dace, a dai-dai lokacin da suke komawa bakin aiki, inda suke ayyukan ban-mamaki, a cewar McConnell ya kuma ce suma zasu yi hakan a yau Litinin.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG