Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Lashi Takobi Sai Ya Sake Maida Takunkumai A Kan Iran


Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump

Shugaban Amurka Donald Trump ya fada a jiya Asabar cewa zai jarraba daukar wani mataki mai tsarkakiya na maido da takunkuman Majalisar Dinkin Duniya a kan Iran, bayan kwamitin sulhun majalisar ya yi watsi da bukatar Washington na kara lokacin haramcin hada hadar makamai a kan Jamhuriyar Islamiya.

“Zamu sake komawa baya” inji shugaban Trump, yana nuni da batun da ake takaddama a kai cewa har yanzu Amurka na cikin yarjejeniyar nukiliyar Iran ta shekarar 2015, duk da janyewa da Trump din ya yi daga yarjejeniyar, kuma haka zai sa ya sake maido da takunkuman, muddin Iran ta bijirewa sharudan yarjejeniyar.

Shugaban kasar ya ce Amurka zata dauki mataki a kan batun a mako mai zuwa.

Trump ya kuma fada a wani taron manema labarai a wurin wani wasan kwallon gulf mallakar sa a Bedminster a jihar New Jersey cewa ba zai halarci taron kolen nan da takwarar sa na Rasha Vladmir Putin ya kira ba tare da Iran.

A ranar Juma’a ne Putin ya kira taron kole ta yanar gizo tsakanin shugabanin kasashe masu kujerun dindindin a kwamitin sulhun MDD tare da kasashen Jamus da Iran a kan yiwuwar kara lokacin haramcin hada hadar makamai a kan Tehran.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG