Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Musanta Rahotannin Zai Kori Rex Tillerson


Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana rahotannin da ke cewa yana kokarin tilastawa sakataren harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson, ya ajiye aikinsa, a matsayin labaran bogi.

Jiya Juma’a shugaba Trump ya kafe ta shafinsa na Twitter yana mai cewa, “kafofin yada labarai na cewa na kori Rex Tillerson, ko yana kan hanyarsa ta barin aiki – LABARAN BOGI! Ba zai bar aikinsa ba, kuma yayin da mukan sami rashin daidaito kan wasu batutuwa, nine mai yanke hukuncin karshe, muna aiki tare kuma Amurka ta dawo da mutuncinta.”

Ranar Alhamis din da ta gabata ne kafofin yada labarai suka rawaito wani babban jami’in gwamnati na cewa, cikin ‘yan makonni masu zuwa shugaban kasa zai iya maye gurbin Tillerson da shugaban hukumar leken asirin Amurka ta CIA Darakta Mike Pompeo. Sai dai baki ‘daya fadar White House da ma’aikatar harkokin waje sun musunta wannan rahoto.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG