Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Samu Ribar Kudi Dala 150 a Shekarar 2005


Trump

Fadar White House ta fitar da wata sanarwar dake cewa Shugaba Donald Trump ya samu ribar sama dala miliyan 150 a shekarar 2005 kuma ya biya harajin dala miliyan 38.

Sanarwar ta caccaki gidan talabijin din da ya bada rahoton cewa kudin harajin da shugaban ya biya ya sabawa doka.

Sanarwar, wadda ta fito da yammacin jiya talata, an bada ita ne jim kadan kafin wani rahoton da gidan talabijin na MNSBC, ya bayyana a cikin shirin Rachel Maddow wanda ta bada wannan bayanin dake kunshe cikin shafi biyu na harajin Trump na shekarar 2005.

Ta ce wani mai sharhi akan harkokin haraji ne ya bada wannan bayanin.

Johnston ya shaidawa Maddow cewa yasamu wadannan bayanan ne cikin akwatin karban sakonninsa na gidan waya, kuma bai san ko wanene ya aiko masa da shi ba.

Maddow tace wannan yasa ta aike da wadannan takardun zuwa fadar White House domin neman Karin bayani.Ta ce amma sai fadar ta gwamnati ta shiga tallata wannan bayanin tun ma kafin ta fara gabatar da nata shirin a cikin daren jiya talata.

Facebook Forum

Bidiyo

Yadda Wani Mutum Ya Mari Shugaban Faransa Emmanuel Macron
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:37 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Marigayi TB Joshua
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG