Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Takarar Shugabancin Faransa Ya Nemi Afuwa Kan Wasu Kalamai


Francios Fillon
Francios Fillon

Dan takarar shugabancin Faransa Francois Fillon, mai ra'ayin rikau, wanda tuni yake fama da wasu matsaloli, yayi nemi gafara saboda kalaman batunci ga yahudawa da ake zargin jam'iyyarsa tayi kan wani abokin karawarsa Emmanuel Macron.

Fillon yace kullum yana yaki da irin masu wannan ra'ayi, daga nan ya umarci jami'an jam'iyyar ta Republican, su dauki mataki kan duk wanda aka samu yana da hanu a ciki. Wannan itace matsalarsa ta baya bayan nan da ya samu.

Da ana ganin kamar Fillon shine zai lashe zaben kasar, amma yanzu an fi yiwa abokan takararsa Macron da Marie Le Pen mai ra'ayin tsatsaturan ra'yin kishin kasa da wasu suke yiwa fassarar wariya a zaman wadand a suka fi shi karfi.

Yakin neman zabensa da ada yake samun dumbin goyon baya, ya fuskanci koma baya, bisa zargin yana biyan matarsa magudan kudi daga baitul malin-gwamnati kan aiki na bogi, a zaman wata hadimarsa a majalisa.

Fillon dai ya musanta ya aikata wani laifi.

Wata jarida r kasar ta buga wani labarin cewa, Fillon ya kuma karbi kayuatar "kot" (coat-suits) biyu daga wani kamfanin dinka sutura, wanda kudinsu ya zarce ka'idar kyauta da za'a iya baiwa dan takarar shugaban kasa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG