Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Tambayi Comey Ko Ana Gudanar Da Bincike a Kansa


A jiya Alhamis ne shugaban Amurka Donald Trump ya fito ‘karara ya fadi cewa a baya ya tambayi shugaban hukumar bincike ta FBI kan cewa ko ana gudanar da bincike akansa.

Ranar Talatar da ta gabata ne Trump ya sallami daraktan hukumar FBI James Comey, wanda hakan ya yi sanadiyyar kace-nace ga ‘yan siyasar Amurka, yayin da wasu ke nuna damuwa game da tsarin mulki.

A wata hira da Trump ya yi da gidan talabijin na NBC News, yace ya tambayi tsohon shugaban hukumar FBI Comey, cewa “Idan da hali, ko zaka iya sanar da ni ko shin ana bincikata? Sai Comey yace baka cikin wani bincike.”

Cikin hirar da aka yi da Trump a talabijin, ya maimaita cewa “bana cikin wani bincike” lokacin da aka tambayeshi cewar James Comey ya bayar da bahasin cewa ana gudanar da bincike alakar tsakanin kwamitin zaben Trump da gwamnatin Rasha a shekarar da ta gabata.

Mai fashin baki kan shari’a Bradley Moss, wanda ya kware kan sha’anin tsaron ‘kasa, ya ce wannan tambaya da shugaban yayi abu ne da bai kamata ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG