Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Yabawa Mexico Da Tare Ayarin Bakin Haure Daga Tsakiyar Amurka


Shugaban Amurka, Donald Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump

Wani ayarin bakin haure daga nahiyar tsakiyar Amurka sun karya katangar kan iyakar Guantemala a jiya Juma’a suna kokarin tasarwa shingen ‘yan sandan a Mexico, wanda gwamnatinta ta yiwa Amurka alkawarin tare ayarin bakin hauren.

Telbijin kasar Mexico ta nuna hotunan daruruwan bakin hauren suna karya katangar kan iyakar Guatemala kana suna wuce a kan gadar dake tsakanin Guatemala din da Mexico. Sai dai bakin hauren sun hadu da ‘yan sanda da suka ja damara a bangaren Mexico.

Wannan ayarin bakin hauren ya tada hankalin shugaban Amurka Donald Trump da sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, wanda ya je birnin Mexico City a jiya Juma’a domin tattaunawa da takwarar aikinsa, ministan harkokin wajen Mexico Luis Videgaray wanda ya lashi takobin daukar matakin a kan ayarin bakin hauren.

Anasa bangare shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana matukar damuwarsa ga wannan labari a wurin wani taron gangamin siyasa.

Yace wasu ne ke son ayarin bakin hauren, akwai kuma masu cewa ba haka tsagaga aka samu bakin hauren ba, akwai kuma dalilan da yasa aka samu ayarin bakin hauren har mutane dubu hudu. Amma dai ina mika godiya ga gwamnatin Mexico saboda sun ta yi kokarin tare ayarin ba ma zasu iya shiga Mexio din ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG