Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Yi Allah Wadai Da Harbe Harben Da Ya Hallaka Mutane A El Paso Da Ohio


Trump

Shugaban ya yi Allah wadai da masu tsattsauran ra’ayin fifita jinsin farar fata, tare da kiran a shiga yin binciken kwakwa, ma duk wani mai neman sayen bindiga.

To amma Trump baya ra’ayin daukar gagarumin mataki a majalisance, na dakile wanzuwar bindiga, inda hakan ya zama abin takaici ga masu ra’ayin daukar wannan matakin.

Haka zalika, bai ma mai da martani ga masu sukarsa ba, wadanda su ka yi zargin cewa zafafan kalamansa na sukar bakin haure, musamman ma ‘yan kasar Mexico, sun taka rawa wajen samar da mummunan yanayi irin wannan.

Trump ya yi jawabin ne a Fadar White House jiya Litini, bayan hare-haren nan biyu da aka kai sa’o’i 13 tsakanin juna, a El Paso da ke jahar Texas da kuma Dayton da ke jahar Ohio.

Wasu daidaikun mahara ne dai su ka kashe jimlar mutane akalla 31 a biranen biyu, baya wasu da dama da su ka ji wa raunuka.

Facebook Forum

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG