Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Zabi Amy Coney Ta Zama Alkalin Babbar Kotun Koli


Shugaban Amurka Donald Trump ya zabi Amy Coney Barrett ta maye gurbin da marigayiya mai shari’a Ruth Bader Ginsburg mai sausaucin ra’ayi, wadda ta ba shi damar sauya akalar kotun da masu ra’ayin mazan jiya gabannin babban zaben shugaban kasa na ranar 3 ga watan Nuwamba.

Trump ya kira Barrett “daya daga cikin ‘yan kasarmu masu hazaka da sanin shari’a,” lokacin da ya sanar da zabin na sa a dakin Rose Garden dake fadar White House, ya kuma ayyana cewa “ta yi matukar cancanta.”

Shugaban kasar ya ce yayi imanin “ya kamata ya zama kai tsaye a kuma tabbatar da ita,” ya yi kira ga ‘yan Majalisa da kafafen yada labarai da su kaucewa kai harin bangarenci ga Barrett.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai, shugaban kasar ya ce zai yi matukar wuya ga ‘yan jam’iyyar Democrat su baiwa wadda ya zaba wahala saboda irin cancantar da take da shi.

Kuri’un jin ra’ayin jama’a sun nuna cewa yawancin Amurkawa, har da ‘yan Majalisun jam’iyyar Democrat suna son duk wanda ya lashe zaben mai zuwa ya zami Alkalin. Da Muryar Amurka ta yi Trump wannan tambaya, cewa ya yi “Bana tunanin sun san Amy,” ya kuma yi hasashen, “Ina tunanin za a kammala kafin zabe.”

Trump ya yi alkawarin zabar mace ta maye gurbin da mai shari’a Ginsburg, wadda ta rasu a makon da ya gabata tana da shekaru 87 a duniya.

Barrett, uwa ce ga ‘ya ‘ya bakwai, idan aka tabbatar da ita, za ta zamanto uwa ta farko mai kananan yara ‘yan makaranta da ta taba zama Alkalin babbar kotun Amurka, mai shekaru 48, kuma za ta zamanto mafi kankantar shekaru cikin kotun mai alkalai 9.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG