Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Zama Tsohon Shugaban Amurka Na Farko Da Ya Fuskanci Shari’ar Aikata Laifuka


USA-TRUMP/NEW YORK
USA-TRUMP/NEW YORK

Donald Trump ya zama tsohon shugaban kasar Amurka na farko da zai fuskanci shari'ar aikata laifuka a ranar Litinin, a lokacin da za a fara zabar masu taya Alkali yanke hukunci a kotun Manhattan, a shari'ar tuhumar biyan kudin toshiyar baki ga taurariyar fina finan batsa Stormy Daniels.

WASHINGTON, D. C. - Haka ya zo a daidai lokacin da zaben Amurka ke karatowa kasa da watanni bakwai, yayin da yake fagen daga don neman komawa Fadar White House.

Trump, mai shekaru 77, yana fuskantar wasu kararraki guda uku kan laifukan da ke tattare da takaddamar doka, kuma maiyuwa ba za su faru ba gabanin zaben da ya kasance ‘dan takarar jam'iyyar Republican da ke kalubalantar Shugaba Joe Biden.

TRUMP-STORMY DANIELS
TRUMP-STORMY DANIELS

Biyu daga cikin sauran shari'o'in sun shafi yunkurinsa na yin watsi da kayen da ya sha da neman juyasakamakon zaben 2020, kuma daya ya shafi rike bayanan sirri bayan ya bar ofis a 2021.

Ana zarginsa da laifin zamba kan kudin da lauyansa na wancan lokacin Michael Cohen ya biya Stormy Daniels, a kwanakin yakin neman zaben shugaban kasa na 2016, don toshiyar baki kan mu’amula da ya yi da ita a 2006, a wani otal mai suna Lake Tahoe.

Trump ya musanta faruwar wannan alaka. A bara kuma ya amsa bai aikata laifuffuka 34 ba na karya a bayanan kasuwancinsa a shari’ar da lauyan gundumar Manhattan Alvin Bragg ‘dan jam’iyyar Democrat ya gabatar a kotun jihar New York, wanda hukunci ba zai hana Trump tsayawa takara ko kuma hana shi hawamulki ba.

Ya bayyana cewa dukkan laifukan da ake tuhumarsa ana yinsu ne don neman cutar da shi a siyasance, kamar yadda ya yi gargadin cewa zai mayar da martani kan abokan hamayyarsa ciki har da Biden, idan ya sake samun shugabancin kasar.

Wasu masana harkokin shari'a sun ce shari'ar da ta mayar da hankali kan lalata a wajen aure, ba ta da kima kan sauran tuhume-tuhumen da Trump da Trump ke fuskanta.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG