Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Yana Shirin Rufe Iyakar Amurka Da Mexico


Shugaba Trump

A cikin wasu jerin sakwannin Twitter, Trump ya yi kira da a canja dokar bakin hauren kasar, wanda ya kira da abar kunya.

Kalaman na shi suna zuwa ne yayain da rufe wani bangaren gwamnatin Amurka ke shiga kwana na cikon bakwai sakamakon rashin amincewa da bukatar Trump a kan kasasfin kudin kasar, inda ya bukaci dala biliyon biyar domin gina Katanga, lamarin da ‘yan majalisa na Democrats suka bada shawara kara karafafa tsaron kan iyakar baki daya amma suka kalubaknci gina katangar.

Rufe iyakar Amurka da Mexico dai yana nufin za a samu tsaiko a kan huldar kasashen biyu wanda ke haifar da cinikin dala biliyon daya da miliyon dari shida da tamanin a duk rana ta Allah.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG